31 Disamba 2025 - 21:44
Source: Quds
Sama Da Ɗaliban Falasdinu 7,000 Ne Suka Yi Shahada A Shekarar 2025

Ma'aikatar Ilimi da Tarbiya ta Falasdinu ta sanar a cikin wata sanarwa a hukumance cewa tun daga farkon shekarar 2025, ɗalibai 7,488 ne su kai shahada, wasu 10,557 kuma sun ji rauni a hare-haren da sojojin mamaye suka kai a Zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Waɗannan ƙididdiga sun nuna mummunan yanayin take hakki ga tsarin ilimi da kuma kai hari kan makarantu da jami'o'in Falasdinu.

A cewar bayanan da aka bayar a cikin wannan rahoton, mafi yawan waɗanda abin ya shafa na Zirin Gaza ne, inda adadin ɗaliban da suka yi shahada ya kai sama da 7,448, yayin da a Yammacin Kogin Jordan, ɗalibai 38 sun yi shahada, kuma sojojin Isra’ila sun kama wasu 324. Baya ga ɗalibai ma'aikatan ilimi suma an kai musu hari a waɗannan hare-haren; Zuwa yanzu, malamai 415 da ma'aikatan gudanarwa sun yi shahada a Zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan, 912 sun ji rauni, kuma an kama sama da 48 daga cikinsu a Yammacin Kogin Jordan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha